in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya ce babu wanda zai iya hana ci gaban al'ummar kasar Sin
2018-04-04 14:14:15 cri

Da safiyar ranar Talata 20 ga watan nan na Maris ne aka rufe zagayen farko, na taron majalisar wakilan jama'ar kasar Sin karo na 13 a nan birnin Beijing.

A yayin rufe taron, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da jawabi a karon farko, tun bayan da ya sake lashe zaben shugabancin kasar ta Sin.

A cikin jawabin nasa, shugaba Xi ya jaddada cewa, zai ci gaba da aiwatar da ayyukan da kundin tsarin mulkin kasar Sin ya dora masa, yayin da yake kiyaye al'ummar kasa cikin himma da kwazo. Haka kuma, ya yi amanar cewa, babu wanda zai iya hana ci gaban al'ummar kasar Sin, muddin dai 'yan kasar sun hada kai da juna.

Shugaba Xi ya ambaci kalmar "al'umma" sau da dama a yayin da yake jawabi, domin jan hankulan ma'aikatan hukumomin gwamnatin kasarsa, game da bukatar sanya al'ummar kasar a matsayin farko a cikin zukatansu, yayin da suke sauke nauyin dake wuyansu na raya kasa.

Xi Jinping ya maimaita tarihin ci gaban kasar Sin, tun daga tsakiyar karni na 19, yana mai cewa Sinawa sun dukufa wajen neman ci gaba cikin hadin gwiwa, duk da irin dimbin kalubalolin da suka sha fama da su cikin shekaru sama da 170 da suka gabata. Sakamakon hakan a cewarsa, ya zuwa yanzu, an kusa kaiwa ga burin farfadowar kasar Sin. Ya ce a nan gaba, idan har al'ummar kasar kimanin biliyan 1.3 sun ci gaba da dukufa cikin hadin gwiwa, ko shakka babu za a kai ga cimma burin farfadowar kasar baki daya." (Saminu Alhassan, Ahmad Fagam/Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China