in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masu sana'ar fina-finai na Sin da na kasashen ketare sun tattauna kan hada hannu don samar da fina-finai
2018-04-17 14:27:55 cri


An shirya dandalin tattaunawar hadin kai game da shirya fina-finai Jiya Litinin, tsakanin Sin da kasashen ketare a yayin bikin fina-finan kasa da kasa karo na 8 da har yanzu ake gudanarwa a nan birnin Beijing. Dandalin da ya samu halartar masu sana'ar fina-finai da suka fito daga kasashe daban daban, ciki har da daraktan fim na kasar Amurka Rob Minkoff, da shugaban zartaswa na kamfanin Huayi Brothers Wang Zhonglei da dai sauransu.

Wadannan masu sana'ar fina-finai sun taru a gun dandalin tattaunawar, don tattauna manufar hadin kan shirya fina-finai tsakanin kasar Sin da kasashen ketare, tare da nazari da tattauna tsari mai amfani na hadin kan sana'ar fina-finai tsakanin kasa da kasa. Wasu daga cikinsu sun bayyana cewa, idan ana fatan hada kai wajen daukar fina-finai, to akwai bukatar a kawar da cikas a fannin al'adu tsakanin kasashe daban daban, inda suka ce bayyana cewa labaru masu kyau shi ne abin da ya fi muhimmanci a fannin.

A 'yan shekaru da suka gabata, sana'ar fina-finan kasar Sin ta samu saurin ci gaba, majigin nuna fina-finai sun wuce 54000 a kasar, hakan ya sa ta kasance kasar da ta fi yawan majigi a duniya. A shekarar 2017, gaba dayan kudin tikitin fim da aka sayar kasar ya kai RMB biliyan 55.9, yawan mutanen da suka tafi sinima don kallon fim kuwa, ya kai biliyan 1.62. Hakan ya sa kasuwar fina-finan kasar Sin ta jawo hankulan masu sana'ar fina-finai na kasa da kasa da yawa, kana ana ta kara yin hadin gwiwar shirya fina-finai tsakanin Sin da kasashen ketare. Ya zuwa karshen shekarar 2017, kasar Sin ta riga ta sa hannu kan yarjejeniyoyin hadin gwiwa na daukar fina-finai tare da kasashe 20, har ma sana'ar fina-finan kasar Sin da manyan kamfanoni 6 na Hollywood na kasar Amurka sun tabbatar da hanyar hadin kai yadda ya kamata.

Stephen Odell, babban daraktan kamfanin SONY Columbia international, na kasar Amurka, wanda ya taba shiga aikin samar da jerin fina-finai na "Spider-Man" da "Men in Black" ya bayyana a yayin dandalin tattaunawar hadin kan fina-finai tsakanin kasar Sin da kasashen ketare da aka shirya a jiya cewa, yanzu suna da shirin daukar wani fim na carton tare da Sin.

"Fim na nan gaba da za mu hada gwiwa wajen dauka, zai bayyana labari game da kasar Sin. Za mu nemo wasu labarun na hikayar mafari ko na masu halin musamman na kasar Sin, kamar labari game da Dragon. A gani na, kasar Sin na da babbar kasuwa, gaskiya ta samar da dama masu yawa gare mu domin zuba jari kan wasu fina-finan dake bukatar kashe kudi da yawa."

Ko da yake akwai makoma mai kyau wajen hadin kan daukar fina-finai, amma a kullum, ana fuskantar wasu matsaloli a fannin. Daukar fina-finai tare na bukatar a kawar da cikas a fannin al'adu tsakanin kasashe daban daban, kuma kamata ya yi a girmama da kuma bin wasu ka'idojin da suka shafi dokoki, tattalin arziki da kuma al'ummar kasashe daban daban. Kana wajibi ne a daidaita hanyoyin aiki tsakanin masu aikin fina-finai. Rob Minkoff, darankan fim na kasar Amurka, wanda ya taba samar da fina-finan na "The Lion King" da "Kings of Kungfu" da dai sauransu, ya bayyana cewa, cimma nasarar wani fim da aka dauka ta hanyar hadin kai na nuna cewa, an yin hadin kai sosai a fannin kirkirar fim din. Ya ce,

"A yayin da muke tattaunawa kan fina-finai, gaskiya kamata ya yi mu mai da hankali kan masu kallon fina-finai, ta yadda zamu rika la'akari da ko labarun da aka bayyana a cikin fina-finai sun samu amincewa a zukatan jama'ar dake bin al'adu iri daban daban. A shekaru 10 da suka gabata, na iso nan kasar Sin don daukar fina-finai, inda na gano cewa, 'yan kungiyar da nake a kasar Amurka sun hada kai tare da mambobin kungiyoyin kasar Sin sosai. "

Idan an waiwayi kasuwar fina-finan kasar Sin a shekarun nan, za a iya gano cewa, yawan kudin da aka samu wajen nuna fina-finan da aka dauka ta hanyar hadin kai, abun mamaki ne. Shugaban zartaswar kamfanin Huayi Brothers Wang Zhonglei ya bayyana cewa, saurin ci gaban kasuwar fina-finai na jawo hankulan kamfanonin fina-finan kasashen ketare mafi yawa, don nazari kan yadda za a gudanar da hadin kai da kasar Sin yadda ya kamata. Ya ce,

"tun daga farkon shirya fim, ya kamata mu hada kai, misali, mu gayyaci masu sana'ar daga Turai da Amurka don su yi nazari tare da mu, hakan zai sanya fim din da aka dauka tare ya samu karbuwa a kasuwar fina-finan duniya. Na biyu, a gani na, daukar fina-finan carton wata hanya ce mai kyau wajen hadin kan daukar fina-finai, wadda za ta gujewa wasu matsalolin da suka shafi bambancin harsuna, da ra'ayin jama'a da dai sauransu." (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China