in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabar IMF: Takkardamar ciniki zai sanyaya gwiwar masu zuba jari
2018-04-20 11:19:31 cri

A gun taron manema labarai da aka yi na taron shekara-shekara na IMF da Bankin duniya na yanayin bazara na shekarar 2018. Shugabar asusun bada lamuni ta kasa da kasa IMF Madam Christine Lagarde ta bayyana cewa, takkardamar ciniki za ta iya sanyaya gwiwar mazu zuba jari na kasa da kasa.

A wannan rana kuma, Lagarde ta ce, idan kwarin gwiwar masu zuba jari ya ragu sosai, to hakika ba zasu nuna sha'awarsu ta zuba jari ba, hakan kuma zai kawo illa ga cinikayyar duniya da tsarin samar da kayayyaki a duniya. A ganinta, ya kamata kasashe daban-daban su yi imani da hada kai da juna don warware irin wannan matsalar takaddamar ciniki data kunno kai tsakanin bangarorin daban-daban. Ban da wannan kuma, ta karawa jami'an kasashen Sin da Afrika kwarin gwiwa dasu yi amfani da zarafin wannan taro don kara yin cudanya da juna.

Game da jawabin da shugaban kasar Sin ya yi a dandalin tattaunawar Asiya na Boao da aka rufe ba da dadewa ba, Lagarde ta ce, shugaba Xi Jinping ya gabatar da wasu manyan matakai da Sin zata dauka nan gaba na kara bude kofa ga kasashen waje, tana fatan za'a tabbatar da wadannan matakai tun da wuri, saboda a ganinta matakan zasu kawo babban amfani ga tattalin arzikin kasar Sin. (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China