in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamfanin ZTE ya sanar da rashin amincewa da takunkumin da ma'aikatar cinikayya ta Amurka ta sakama masa
2018-04-20 13:11:21 cri

Kamfanin sadarwa na kasar Sin ZTE ya bada sanarwa a yau Juma'a cewa, ZTE ba zai amince da takunkumin da ma'aikatar cinikayyar Amurka ta yanke na hana fitar da kayayyaki ZTE ba,a ganinsa matakin ya kasance rashin adalci ne.

An bada labari cewa, ma'aikatar ta bada wata sanarwa a ranar 16 ga wata cewa, saboda ZTE ta sabawa yarjejeniyar samun daidaituwa tsakaninsa da gwamnatin Amurka, shi ya sa ta yanke shawarar hana fitar da kayayyaki ga ZTE mai wa'adin shekaru 7, abin da ya bayyana cewa a cikin shekaru 7 masu zuwa, kamfanonin Amurka ba za su sayar da wasu kayayyakin sadarwa ga kamfanin ZTE ba.

Game da wannan takunkumi ZTE ya bada sanarwa cewa, wannan umurni dai zai kawo babbar illa ga ZTE har ma ga moriyar wasu kamfanonin Amurka dake hada kai tare da ZTE. Sanarwar ta ce, ZTE zai ci gaba da kokarin warware matsalar ta hanyar tattaunawa, kuma yana da niyyar kiyaye moriyarsa ta ko wata hanya da ta dace a bisa doka. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China