in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An nuna fina-finan kasar Sin da aka fassara su zuwa yaren ketare a bikin nuna fina-finai na Beijing
2018-04-20 19:59:07 cri
An shirya taron bajekolin fina-finai, a gefen babban bikin nuna fina-finai na kasashe daban daban karo na 8 da yake gudana a nan birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin. Taron dai ya gudana ne tsakanin ranekun 18 zuwa 20 ga watan nan da muke ciki. Inda a karon farko cibiyar fassara fina-finai zuwa harsuna daban daban ta kasar Sin, karkashin babbar kungiyar yada labarai ta kasar, ta nuna wasu fina-finan da aka fassara su da kuma nuna su a gidajen telabijin na kasashen waje.

An kafa cibiyar fassara fina-finan ta kasar a watan Janairun shekarar 2014. Kawo yanzu, ta riga ta fassara fina-finan kasar Sin fiye da 300, da wasannin kwaikwayon kasar da ake nuna su ta telabijin, da kuma majigin yara na wasu fiye da babi 7000, zuwa harsuna 23.

Ban da haka, cibiya ta kulla yarjejeniyar hadin gwiwa da manyan kafofin yada labarai na wasu kasashe fiye da 30 daga nahiyoyi daban daban, domin su nuna fina-finai da wasannin kwaikwayon talabijin a wadannan kasashen. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China