Wani kwamiti mai kula da aikin tantance batun tattalin arziki da tsaro tsakanin Amurka da Sin, karkashin laimar majalisun kasar Amurka, ya fitar da wani rahoto a kwanakin baya, inda aka ce mai yiwuwa ne gwamnatin kasar Sin na goyon bayan wasu kamfanonin kasar, a ayyukan leken asiri a fannin kasuwanci, tare da zummar kara karfin kamfanonin, da tabbatar da moriyar gwamnatin, inda aka ambaci sunayen wasu kamfanonin kasar Sin da suka hada da ZTE, Huawei, da Lenovo.
Don gane da wannan zargi, Madam Hua ta ce, idan kasar Amurka ta rika daukar matakai bisa wasu dalilai "marasa tabbas", to, hakan ba wani mataki ne mai nagarta ba, kuma hakan yana da hadari. (Bello Wang)