in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mahukuntan Sin sun amince da tsarin kafa sabon yankin Xiongan
2018-04-20 21:07:50 cri
Kwamitin koli na JKS mai mulkin kasar Sin da majalisar zartaswar kasar, sun amince da babban tsarin kafa yankin Xiongan, yana mai bayyana tsarin da cewa, mataki ne da zai zamo "Gagara gasa a shekaru masu yawa dake tafe."

Wata takardar bayani da kwamitin kolin ya fitar a Juma'ar nan ta bayyana cewa, yankin na Xiongan zai kasance wani wuri mai "matukar daraja a mataki na kasa da kasa", inda zai bi bayan yankin musamman na raya tattalin arziki na Shenzhen, da sabon yankin musamman na Shanghai Pudong.

A watan Afrilun shekarar bara ne dai Sin ta bayyana kafuwar yankin na Xiongan, wanda zai hade gundumomi guda uku dake lardin Hebei, mai nisan kilomita 100 daga kudu maso yammacin birnin Beijing.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China