MDD ta ce karancin ruwan sama a bara ya haifar da fari da ya shafi galibin yankin Sahel, al'amarin da ya jefa mutane sama da miliyan 10 cikin tsananin bukatar abinci a bana.
Kakakin MDD Farhan Haq, ya ruwaito ofishin hukumar dake kula da agajin jin kai na cewa, tuni lokacin bazara dake kai wa har watanni Yuni da Augusta, ya fara tun a watan Maris a wasu yankunan, wanda ya haifar da asarar dabbobi. Abun da ya haifar da matsala fiye da yadda aka saba gani musammam a yankunan da ake kiwo da wadanda ake noma da kiwo.
A cewarsa, baki daya dai, sama da mutane miliyan 10 ne za su bukaci agajin gaggawa na abinci a lokacin bazara, adadin da ya karu kan miliyan 7.1 da ake da shi a yanzu.
Bugu da kari, ya ce yara miliyan 1.6 'yan kasa da shekaru 5 ne ke fama da matsananciyar tamowa, adadin da ya karu kan na bara da kaso 46.
Matsalar ta fi kamari ne a kasashen yankin Sahel da suka hada da Burkina Faso da Senegal da Chadi da Mali. (Fa'iza Mustapha)