Gwamnatin kasar ta tsaida wannan kudurin ne yayin cikakken zama na 3 na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwadago ta kasar karo na 7 da ya gudana a jiya Jumma'a.
KCNA ya kuma ruwaito cewa, ban da wannan, an kuma zartas da wasu matakan da suka hada da rufe filin gwajin makaman nukiliya dake arewacin kasar don tabbatar da dakatar da gwajin makaman baki daya.
Kudurin ya kara da cewa, kasar ba za ta yi amfani da makaman nukiliyar ba muddun ba ta fuskanci barazana ba. Sannan, Kasar ba za ta mika makaman nukiliya da fasahohinta ga kowa ba.
Har ila yau, an tsaida kudurin cewa, za yi amfani da albarkar jama'a da kasar ke da su da albarkatu da kayayyaki wajen raya tattalin arzikin kasar da inganta rayuwar al'ummarta. (Zainab)