in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ayyukan da kasar Sin ta sama da kudaden aiwatarwa sun inganta ci gaban Kenya
2018-04-21 16:28:07 cri

Sakataren ma'aikatar baitulmali da tsare-tsare na Kenya Kamau Thugge, ya ce kayayyakin more rayuwa da kasar Sin ta samar da kudin aiwatarwa a kasar, sun taimaka wajen habaka tattalin arzikin kasar da kaso 5.5 bisa 100 cikin shekaru 5 da suka gabata tun daga shekarar 2013, idan aka kawatanta da kaso 4.5 bisa 100 da ya kasance daga shekarar 2008 zuwa ta 2012.

Sakataren ya ce daga matsayin Kenya da kasar Sin ta yi a bara zuwa muhimmiyar abokiyar hulda, wajen aiwatar da manyan manufofin kasar 4, zai kara zurfafa hadin kai tsakanin kasashen biyu.

Ya kuma yi kira ga kamfanonin kasar Sin da su hada hannu da takwarorinsu na kasar, domin cin gajiyar taimakon da gwamnatin ke bayarwa dake mayar da hankali wajen cimma wadancan muradun 4.

Manufofin 4, tsari ne na ayyukan ci gaba cikin shekaru 5 da shugaban kasar Uhuru Kenyatta ya gabatar domin sauya rayuwar jama'ar kasar ta hanyar samar da kayayyaki da wadatar abinci da inshorar lafiya da kuma gidaje masu rahusa, domin dorawa kan ayyukansa a wa'adin mulkinsa na karshe da zai kare a shekarar 2022.

Sakataren ya ce an samu habakar tattalin arzikin ne saboda ayyukan more rayuwa da kasar Sin ta samar da kudin aiwatarwa, wanda kuma ya taimakawa kasar samun karin kudin shigar ko wane dan kasa a cikin shekara, daga dala 1,000 a shekarar 2013 zuwa dala 1,740 a bana. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China