in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yabawa kokarin kasar Sin na kare tsarin noma na gargajiya
2018-04-21 16:42:42 cri

Hukumar kula da samar da abinci da ayyukan gona na MDD ta FAO, ta bayyana kasar Sin a matsayin kasar da kawo yanzu, ta fi ko wace a duniya wajen kare tsarin ayyukan gona na gargajiya.

Jami'in hukumar Mauro Angoletti ne ya bayyana haka, yayin wani muhimmin taron kasa da kasa kan alkinta tsarin noma da ya gudana a birnin Roma.

Jami'in ya shaidawa Xinhua cewa, gamnatin kasar Sin na daya daga cikin manyan masu goyon bayan ayyukan hukumar FAO kuma tana da gogewa mai amfani da za ta iya koyawa sauran sassan duniya.

Yayin taron, an ware wasu yankuna 13 na alkinta ayyukan gona na gargajiya, inda 4 daga cikinsu suka kasance na kasar Sin. Da wadannan sabbin, yanzu adadinsu ya kai 50 a fadin duniya, inda 15 suka kasance a kasar Sin, al'amarin da ya sa kasar zama kasa mafi yawan wadanan wurare a duniya.

Mataimakin shugaban hukumar kula da harkokin gona da na karkara ta kasar Sin Zhang Taolin, ya ce gwamnatin kasar Sin ta dauki batun alkintawa da kare tsarukan noma na gargajiya da muhimmanci, wanda ya ce ya na fito da muhimmancin noman gargajiya da inganta zamanantar da tsarin da samar da ci gaba mai dorewa ga harkokin gona tare da jajircewa wajen tabbatar da ba a yar da al'adar noma ba. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China