in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya tsara tsarin raya yanar gizo da sadarwa na kasar Sin
2018-04-21 17:36:21 cri

An gudanar da taron kula da tsaron yanar gizo da sadarwa na kasar Sin daga jiya Jumma'a zuwa yau Asabar a nan birnin Beijing, inda babban sakataren kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin kuma shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci taron tare da gabatar da jawabi.

Shugaba Xi Jinping ya jaddada cewa, aikin sadarwa ya samar da babbar dama ga raya al'ummar kasar Sin, inda ya ce dole ne a rike damar raya aikin sadarwa, da kara fadakar da abubuwan da suka dace, da tabbatar da tsaron yanar gizo, da sa kaimi ga raya fasahohin sadarwa, da taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa tattalin arziki da zamantakewar al'umma, da kara hada kan sojoji da jama'a a fannin raya yanar gizo, da shiga yunkurin sarrafa yanayin yanar gizo, gami da yin kirkire-kirkire wajen gina kasa mai karfi a fannin yanar gizo, a kokarin samar da sabuwar gudummawa wajen raya al'ummar kasa mai wadata da raya tsarin gurguzu na musamman na kasar Sin a sabon zamani da kuma cimma burin kasar Sin na farfado da al'ummarta.

Xi Jinping ya kuma kara da cewa, sa kaimi ga raya tsarin sarrafa yanar gizo na duniya ya dace da yanayin duniya da bukatun jama'ar duniya. Kuma ya kamata a yi amfani da damar raya shawarar "ziri daya da hanya daya" da sauran shirye-shirye wajen kara yin hadin gwiwa da kasashen da suke bin shawarar, musamman ma kasashe masu tasowa, wajen raya tsarin yanar gizo da tattalin arziki ta hanyar yanar gizo da kiyaye tsaron yanar gizo don raya hanyar siliki ta sadarwar zamani ta karni na 21. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China