in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An shirya bikin fina-finai na kasa da kasa na Beijing karo na 8
2018-04-26 14:39:10 cri

A ranar Litinin 16 ga watan ne aka bude taron dandalin tattaunawa, game da hadin kai a fannin shirya fina-finai tsakanin Sin da kasashen ketare, a yayin bikin fina-finan kasa da kasa karo na 8 da ya gudana a nan birnin Beijing. An dai rufe wannan taro ne a ranar Lahadi 22 ga wata.

Dandalin dai ya samu halartar masu sana'ar fina-finai, da suka fito daga kasashe daban daban, ciki hadda daya daga manyan daraktocin fim na kasar Amurka Rob Minkoff, da shugaban zartaswa na kamfanin "Huayi Brothers" Wang Zhonglei da dai sauransu.

Wadannan masu sana'ar fina-finai sun taru ne a dandalin tattaunawar, don tattauna manufar hadin kai ta shirya fina-finai tsakanin kasar Sin da kasashen ketare, tare da nazari da tattauna tsari mai amfani, na hadin kai a sana'ar fina-finai tsakanin kasa da kasa.

Wasu daga cikinsu sun nuna cewa, idan ana fatan hada kai wajen shirya fina-finai, to akwai bukatar a kawar da cikas a fannin al'adu tsakanin kasashe daban daban, suna masu cewa labaru masu kyau su ne abu mafi muhimmanci a wannan fannin.

A 'yan shekaru da suka gabata, sana'ar fina-finan kasar Sin ta samu saurin ci gaba, inda wuraren nuna fina-finai sun wuce 54,000 a kasar. Hakan ya sa ta kasance kasar da ta fi yawan wuraren kallon fina finai a dukkanin duniya.

A shekarar 2017, bisa jimilla, kudin tikitin kallon fina finai da aka sayar a kasar, ya kai RMB biliyan 55.9, kuma yawan mutanen da suka shiga sinima don kallon fim ya kai biliyan 1.62. Hakan ya sa kasuwar fina-finan kasar Sin ke jawo hankulan masu sana'ar fina-finai na kasa da kasa da yawa, kana ana ta kara yin hadin gwiwar shirya fina-finai tsakanin Sin da kasashen ketare.

Ya zuwa karshen shekarar 2017, kasar Sin ta riga ta sa hannu kan yarjejeniyoyin hadin gwiwa na daukar fina-finai tare da kasashe 20, yayin da kuma sana'ar fina-finan kasar Sin, da manyan kamfanoni 6 na Hollywood na kasar Amurka suka cimma hanyar hadin kai tsakaninsu.

A yayin bikin, an fid da fitattun fina-finai da aka baiwa lambobin yabo na Tiantan, an kuma a nuna fina-finai masu kyau na kasar Sin da ma na sauran kasashen duniya. (Saminu Hassan, Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China