in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Neymar ya bayyana tsoron da yake ji game da komawa fagen tamaula
2018-05-17 15:07:12 cri

Dan wasan Brazil da PSG Neymar, ya bayyana fatan sa na samun cikakkiyar warwarewa, kafin bude kasar cin kofin duniya dake tafe nan da 'yan makwanni.

Neymar ya bar taka leda ne tun cikin watan Fabarairu, lokacin da ya samu rauni a kafa, aka kuma yi masa aikin tiyata a birnin Belo Horizonte na kasar Brazil a ranar 3 ga watan Maris, kafin komawar sa birni Paris cikin makon da ya gabata domin ci gaba da murmurewa.

Da yake zantawa da wata kafar watsa labarai, Neymar mai shekaru 26 da haihuwa, ya ce "Na fara tafiya da kafa ta, amma ina jin tsoron sake komawa kwallo". Ya ce "ina bukatar samun karfin zuciya na kauda tsoron da nake ji a rai na, ta yadda zan iya komawa fagen kwallo, kafin a fara buga gasar cin kofin duniya."

Kafin hakan dai Neymar ya ce ga alama ba zai bugawa Paris Saint-Germain wani wasa ba, a ragowar wasannin kakar bana, duba da cewa PSGn za ta yi wasan ta na karshe ne a kakar bana, tsakanin ta da Caen a ranar 19 ga watan Mayu.

A farkon watan nan ne likitan kungiyar kwallon kafa ta Brazil Rodrigo Lasmar, ya yi hasashen cewa, Neymar zai murmure sarai, kafin bude gasar cin kofin duniya dake tafe a watan Yuni.

A kakar wasa ta bana, Neymar ya ci kwallaye 28, ya kuma taimaka wajen cin wasu kwallayen 16, cikin wasannin da PSG ta buga, tun bayan barin sa Barcelona, inda a watan Agustan bara, aka yi cinikin komawar sa PSG kan kudi har Euro miliyan 222.

Da yake tsokaci game da zaman sa a Barcelona, Neymar ya ce kakar wasa 4 da ya yi a Camp Nou na da mana'ar gaske, musamman idan ya tuna yadda ya taka leda tare da Lionel Messi da Luis Suarez. Ya ce ba sa rabuwa sam, kuma ko kallon juna suka yi yayin da ake taka leda, sun san abun da ya dace su yi domin samun nasara.

Shugaba Temer na Brazil ya bukaci yan wasan kwallon kafan kasarsa su lashe kofin duniya

Shugaban kasar Brazil Michel Temer ya bukaci tawagar 'yan wasan kwallon kafar kasar dasu lashe kofin gasar kwallon kafan duniya ta FIFA dake tafe.

A sanarwar da ya wallafa ta shafinsa na Twitter, shugaba Temer yayi jawabi game da gasar kwallon kafan duniyar ne bayan da kungiyar wasan kwallon kafan kasar ta fitar da sunayen karshe na 'yan wasan 23 wadanda zasu wakilci kasar a gasar ta FIFA.

Da yake jawabi ga tawagar 'yan wasan kasar da kociyan kungiyar Tite, shugaban kasar yace, tuni suka tanadi 'yan wasan da zasu halarci gasar kwallon kafan duniyar a kasar Rasha. Yace a yanzu sun shirye tsab domin zuwa kasar ta Rasha waddda zata karbi bakunci wasan, don haka ya umarci tawagar 'yan wasan na kasarsa dasu jajurce don daukowa kasar tasu kofin.

Wasan kwallon kafa yana da matukar daraja ga kasar ta Brazil. Kasar ta taba lashe kofin duniya har sau biyar; da suka hada da na shekarar 1958, 1962, 1970, 1994 da shekarar 2002, kuma kasar ce ta karbi bakuncin gasar wasan kwallon kafan duniya a shekarar 2014, inda kungiyar wasan kwallon kafan ta Brazil ta kwashi kashinta a hannun Jamus a wasan kusa da na karshe inda ta samu sakamako mai ban haushi da ci 7 da 1.

Tun bayan da kasar ta samu wannan mummunan sakamako a gasar cin kofin duniyar, tagawar 'yan wasan ta Brazil take ta kokarin dawo da martabarta a fagen wasannin. Yan wasa 6 ne kadai zasu halarci gasar daga cikin 'yan wasan 13 da suka halarci gasar cin kofin duniyar na 2014 da basu samu nasara ba.

Brazil zata buga wasanta na farko a gasar kofin duniyar ta 2018, inda zata fafata da Switzerland a ranar 7 ga watan Mayu. Sauran wasannin da zata buga a rukunin farko sun hada da wasa tsakaninta da Costa Rica, a ranar 22 ga watan Yuni, sai kuma wasan da zata buga da Serbia, a ranar 27 ga watan Yuni.

Fagner zai maye gurbin Danis Alves a kungiyar kasar Brazil

Rahotanni daga hukumar dake lura da harkar wasan kwallon kafa ta kasar Brazil, na cewa akwai yiwuwar dan wasan kasar Fagner Conserva Lemos, ya maye gurbin Dani Alves, a gasar cikin kofin kwallon kafa ta duniya dake tafe a Rasha.

Wata sanarwa daga hukumar ta bayyana cewa, likitan kungiyar Rodrigo Lasmar, ya yi amannar cewa, Fagner na da cikakkiyar lafiyar da zai iya buga gasar ta cin kofin duniya, wadda za fara a ranar 14 ga watan Yuni. Kafin hakan an riga an fidda tsammanin dawowar Fagner, sakamakon rauni da ya ji a cinyar sa a ranar 29 ga watan Afirilu.

Ana sa ran nan da 'yan kwanaki kocin kungiyar Tite, zai sanar da jerin 'yan wasan Brazil da za su wakilci kasar a gasar dake tafe.

Brazil dai na cikin rukuni na E, tare da Switzerland, da Costa Rica, da Serbia. Za kuma ta buga wasan farko da Switzerland, a ranar 17 ga watan Yuni.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China