180612-Zantawa-da-Umar-Gimba-a-ziyararsa-a-birnin-Beijing.m4a
|
A wannan mako, shirin Sin da Afirka ya karbi bakuncin wata tawagar 'yan jaridu daga kafafen yada labaru daga tarayyar Najeriya wadanda suka kawo ziyarar aiki nan birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, tagawar ta ziyarci gidan radiyon kasar Sin wato CRI. Wakilinmu Ahmad Fagam ya samu tattaunawa da guda daga cikin 'yan jaridun wato Umar Gimba, wanda ke aiki da gidan talabijin na Channels TV dake Najeriya, inda ya tambaye shi game da makasudin ziyarar tasu da ma sauran batutuwa da suka shafi dangantaka tsakanin kasar Sin da Najeriya har ma da sauran kasashen Afrika, ga cikakkiyar hirar tamu.