Rahotanni na cewa, a yau ne shugaban kasar Koriya ta arewa Kim Jung-un ya gana da takwaransa na kasar Amurka Donald Trump karon farko a tarihi a Singapore, inda suka yi shawarwari kan batun kawar da makaman nukiliya a zirin Koriya da rage tsamin dangantakar dake tsakaninsu. (Amina Xu)