in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin kasa da kasa sun yi farin ciki kan sakamakon da aka samu cikin ganawar Trump da Kim Jung-un
2018-06-13 13:28:19 cri

Shugaban Koriya ta arewa Kim Jung-un ya gana da takwaransa na kasar Amurka Donald Trump a jiya 12 ga wata a Singapore, tare da sa hannu kan wata hadaddiyar yarjejeniya. Shugabannin kasashen duniya sun gamsu sosai ga ci gaban da aka samu.

Babban sakataren MDD Antonio Guterres ta bakin kakakinsa, ya ba da wata sanarwa a wannan rana cewa, yana maraba da ganawar da aka gudana a wannan rana, tare da yin kira ga bangarori masu ruwa da tsaki da su yi amfani da wannan dama mai kyau don tabbatar da kawar da makaman nukiliya a zirin.

Wakiliya mai kula da harkokin waje da manufar tsaro na EU Federica Mogherini ta ba da sanarwa cewa, ganawar tasu a wannan karo ta tabbatar da cewa matakin diplomasiyya hanya daya tilo ne wajen wanzar da zaman lafiya a zirin.

Ministan harkokin waje na kasar Rasha Sergei Lavrov ya ce, ganawar da aka yi ta ba da sako mai yakini. Shugaba Trump ya taba nuna cewa, zai dakatar da atisayen soja cikin hadin kai da Koriya ta kudu bayan ya gana da Kim Jung-un, shi ya nuna farin ciki sosai ga lamarin.

Ban da wannan kuma, shugaban Koriya ta kudu Moon Jae-in ta bayyana matukar farin ciki ga ganawar a wannan rana tare da taya murnar cimma nasarar a ganawa. (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China