in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Muhimmancin ganawar shugabannin kasashen Koriya ta arewa da Amurka ga zaman lafiyar duniya
2018-06-13 17:40:20 cri

A jiya Talata ne, shugaban kasar Koriya ta arewa Kim Jung Un da takwaransa na kasar Amurka Donald Trump suka gana a kasar Singapore, ganawa ta farko a tsakanin shugabanni masu ci na kasashen biyu. Bayan ganawar, shugabannin biyu sun kuma rattaba hannu kan wata yarjejeniya.

Daga bisani sun kuma sanya hannu kan wata yarjejeniya mai matukar muhimmanci, wadda ta shafi fannoni daban daban. Sun kuma kuduri aniyar yin watsi da abubuwan da suka faru a baya domin rattaba hannu kan wannan yarjejeniya mai ma'ana a tarihi. Duniya baki daya za ta ga babban canji.

Rahotanni na cewa, yarjejeniyar ta kunshi alkawarin da Amurka da Koriya ta arewa suka yi na kafa sabuwar dangantaka a tsakanin kasashen biyu bisa burin jama'arsu na neman zaman lafiya da samun wadata. Ban da wannan, Amurka da Koriya ta arewa za su hada kai don kafa wani tsarin zaman lafiya mai dorewa a zirin Koriya.

Kasar Koriya ta arewa kuma ta nanata Sanarwar Panmunjomon da aka fitar a ranar 27 ga watan Afrilu na shekarar 2018, inda ta yi alkawarin cewa, za ta yi kokarin cimma burin kawar da makaman nukiliya a zirin koriya. Bugu da kari, Amurka da Koriya ta arewa sun yi alkawarin cewa, za su gano gawawwakin fursunonin yaki da wadanda suka bace a lokacin yakin Koriya da aka gwabza daga shekarar 1950 zuwa 1953, da gaggauta dawo da wadanda tuni aka gano.

Haka zakila, a yayin taron manema labarai da Shugaba Trump ya shirya, ya nuna godiya ga kokarin da bangarori daban daban ciki har da shugaban kasar Sin Xi Jinping suka yi domin ganin an samu zaman lafiya a zirin Koriya. Ya kuma bayyana cewa, zai dakatar da atisayen soja tare da kasar Koriya ta kudu.

Masu sharhi na fatan shugabannin za su martaba tanade-tanaden dake cikin yarjejeniyar, matakin da ake fatan kawo alheri ga dukkan bangarorin da wannan batu ya shafa, kana daga karshe a samu zaman lafiya a duniya. (Ahmed, Ibrahim/ Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China