A jawabin na sa, shugaba Putin ya yi maraba da zuwan daukacin 'yan wasa da, jami'ai, da masoya kwallon kafa kasar ta Rasha, yana mai jinjinawa kwazon da FIFA, da hadin gwiwar gwamnatin sa, wajen ganin dukkanin shirye shirye sun kammala yadda ya kamata.
Shugaba Putin ya ce Rasha ta shiryawa wannan gasa ta cin kofin kwallon kafa ta duniya, ta hanyar samar da tsaro da sauran abubuwa da masu sha'awar kwallon kafar za su bukata. Ya ce gasar cin kofin duniya na da matukar muhimmanci ga kasarsa, kuma zuwan lokacin da za a fara gudanar da ita a Rashan, wani mafarki ne da ya tabbata ga daukacin 'yan kasar.
A daren gobe Alhamis bisa agogon kasar ta Rasha ne za a bude gasar ta cin kofin duniya na bana, inda mai masaukin baki Rasha za ta kece raini da kasar Saudi a wasan farko.