in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rukunin masana'antun dake ketare sun kara bunkasa hadin gwiwar Sin da Afirka a fannin masana'antu
2018-06-15 17:01:50 cri



A watan Oktoban wannan shekarar ce rukunin masana'antun hakar ma'adinai na Sin da Uganda zai fara aiki, abin da ke zama misali na hadin gwiwar kasashen biyu a fannin yawan kayayyakin da bangaren ke samarwa .

Lyu Weidong, shugaban rukunin kamfanin samar da makamashi na Guangzhou DongSong ya ce, za a yi amfani da kwarewar da kasar Sin take da shi a fannin raya masana'antu da kula da gurbatar muhalli, yayin tafiyar da rukunin masana'antu, da ma matakan kare muhalli da sauransu.

Lyu Weidong ya ce a baya, wasu sassan kasar Sin sun bunkasa tattalin arziki ba tare da la'akari da batun kare muhalli ba, don haka sun koyi darasi daga kura-kuran da aka tafba a baya, da farko za a mayar da hankali ne ga batun da ya shafi kare muhalli, duk da yawan jarin da za a zuba.

Yanzu haka jarin dala miliyan 620 da aka zuba, rukunin masana'antun dake gundumar Tororo a kasar Uganda ya kunshi tashoshin sarrafa albarkatu, da samar da takin zamani ko gorar ruwa ko gwangwanaye. Haka kuma akwai kamfanin yin bulo da bangaren samar da daben daki, dukkansu suna amfani da kwanon gorar ruwa ne da tashar sarrafa masai wadda ke sake tace ruwan da ake amfani da shi a masana'antar, baya ga iskar gas da tururin da ake sabuntawa.

Jami'in ya ce, rukunin masana'antu ne da ya kunshi komai da komai, wanda baya ga kara yawan albaraktun da ake samarwa, ya kuma magance abubuwan dake yiwa muhalli illa.

Yanzu haka wasu kasashen Afirka sun himmatu wajen gina rukunin masana'atu da yankunan tattalin arziki na musamman, domin samar da managartan hanyoyin raya tattalin arziki da jin dadin jama'a, ta hanyar amfani da kwarewa da jarin da kasar Sin take zubawa a irin wadannan kasashe.

Shugaban rukunin kamfanonin Guangdong New South, kana mai kula da yankin tattalin arziki na musamman na Ogun da Guangdong dake jihar Ogun a tarayyar Najeriya wanda ya kunshi kamfanoni kimanin 26 a filin da ya kai murabba'in girman kilomita 2.24 Zhu Layi, ya ce, rukunin ya tara kudaden da suka kai Yuan biliyan 1.5 kwatankwacin dala miliyan 234, sannan ya dauki ma'aikatan yankin kusan 5,000.

Manyan kamfanonin dake cikin rukunin masana'atun sun hada da Goodwin Ceramic, babban kamfanin samar da kayan karau a Afirka, wanda a kullum yake samar da kayan karau da ya kai mita 120,000. Akwai kuma kamfanin Hewang Packaging and Printing FZE, mai kula da harkokin kunshin kaya da dab'i dake tarayyar Najeriya, wanda ke samar da takardun da suka kai 600,000 a ko wace rana, dukkansu an gina su ne da jarin kasar Sin.

Alkaluman hukumar kididdiga ta kasa sun nuna cewa, a rubu'in farko na wannan shekara, adadin cinikayya tsakanin Sin da Afirka ta karu da kaso 12.4 cikin 100 kan na shekarar da ta gabata. Darajar jarin da Sin ta zuba a Afirka ya kai sama da dala biliyan 100, kana ta gina sama da yankunan tattalin arziki 20 a nahiyar, baya ga wasu da ake shirin ginawa.

Kasar Sin tana dora muhimmanci kan muhimman kayayyakin more rayuwa da yanayin zuba jari kafin ta gina yankunan tattalin arziki, lamarin dake janyo hankulan masu sha'awar zuba jari na ketare da kara samarwa jama'ar wurin ayyukan yi, kuma galibin al'ummar Afirka sun yi imanin cewa, dabarun kasar Sin abin koyi ne.

Yayin da ake kara samun kamfanonin kasar Sin dake zuba jari a kasar Habasha, kamfanonin suna kuma kiyaye hakkokin jama'a da dokokin kasuwanci na kasa da kasa a lokacin da suke zuba jari da kuma gina rukunin masana'antu a nahiyar Afirka. Sabbin rukunonin masana'antun da aka gina, za su kara bunkasa alakar Sin da kasashen Afirka.

Kamfanonin Sin sun yi imanin cewa, akwai damammaki masu tarin yawa a alakar sassan biyu, duba da damammakin dake makare a kasuwannin nahiyar ta Afirka.

Yanzu haka dai rukunin kamfanonin DongSong na kasar Sin yana shirin kaddamar da ayyukan raya makamashi a Kamaru da Mozambique cikin shekaru 3 masu zuwa, Shi ma rukunin kamfanin New South yana shirin gina rukunonin masana'antu 10 da cibiyoyin kiwon lafiya 10 a Afirka cikin shekaru 5 masu zuwa. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China