in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilin MDD dake Sin ya yabawa gudunmawar da Sin ke bayarwa a hadin gwiwar kasashe masu tasowa
2018-06-15 13:54:21 cri

Jiya Alhamis ne wakilin MDD dake kasar Sin Nicholas Rosellini, ya gabatar da jawabi game da gudunmawar da Sin take bayarwa, ta fuskar hadin gwiwar kasa da kasa a sabon karni, a cibiyar CCG dake birnin Beijing. A cikin jawabin nasa, Mr. Rosellini ya jinjinawa gudunmawar da Sin take bayarwa a fannin hadin gwiwar kasashe maso tasowa.

Ya ce, Sin ta samar da kudin tallafi na dala biliyan 60 a cikin shekaru 40 da suka gabata, don tallafawa hadin gwiwar kasashe maso tasowa, adadin da ya karu da kashi 10 cikin 100 a ko wace shekara tun daga shekarar 2003. An kiyasta cewa, yawan kudin tallafi da Sin ta samarwa kasashen waje ya kai dala biliyan 5 da miliyan 800 a shekarar 2016, wanda shi ne ke matsayi na 7 a duniya.

Ban da wannan kuma, Rosellini ya ambaci shawarar da Sin ta gabatar ta "Zirin daya da hanya daya". A ganinsa, wannan shawara za ta iya zama wani muhimmin abin koyi ta bangaren hadin gwiwar kasa da kasa. Ya kuma kara da cewa, shawarar ta ba da muhimmin taimako ga bunkasuwar shiyyar, da dunkunlewar shiyyar bai daya, ta hanyar hada juna ta fannonin tattalin arziki da zaman al'umma da hada-hadar kudi. (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China