IMF ta bayar da sanarwa a wannan rana, inda ta jaddada cewa, kamata ya yi a gudanar da tattalin arzikin duniya bisa tsarin ciniki a bude, cikin adalci da bin ka'idoji, amma manufar ciniki, da matakan da Amurka ke dauka, sun kawo damuwa ga bangarori daban daban, saboda tasiri maras kyau da za su yi wa Amurkar da ma abokan cinikayyarta. (Bilkisu)