Sa'annan a rukuni na B, a birnin Saint Petersburg, Iran ta doke Morocco da ci daya da nema, inda dan wasan Morocco Aziz Bouhaddouz ya buga kwallo da ka cikin ragarsu, abun da ya jawo nasarar da Iran ta samu, wadda kuma ta zama nasara ta biyu da ta taba samu a tarihinta na halartar gasar cin kofin duniya.
Har wa yau, a wata fafatawa ta daban a rukunin B a birnin Sochi, Spaniya da Portugal sun yi canjaras da ci uku da uku, inda shahararren dan wasan kwallon kafar Portugal Cristiano Ronaldo, ya zura kwallaye uku shi kadai.(Murtala Zhang)