Tawagar kasar Sin a AU ce ta shirya wani bulaguro da ya hada jami'an AU da sauran jami'an diflomasiyyar kasashen nahiyar, cikin jirgin kasan da ya hada Habasha da Djibouti.
Shugaban Tawagar ta kasar Sin Kuang Weilin, ya ce tafiyar wadda ta hada da ziyartar yankin masana'antu da kasar Sin ta gina a garin Adama dake da nisan kilomita 80 daga birnin Addis Ababa na Habasha, na da nufin ba matafiyan damar ganewa idonsu ayyukan da aka aiwatar karkashin hadin gwiwar kasar Sin da nahiyar Afrika da kuma shawarar 'Ziri Daya da Hanya Daya'.
A cewar Rossette Nyirinkindi Kataungye, mashawarcin AU kan hadin kan nahiyar, layin dogon misali ne na kudurin kasar Sin, na taimakawa nahiyar Afrika cimma burinta na samun ci gaba da kuma dunkulewa wuri guda. (Fa'iza Mustapha)