in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan mutanen da ake zargin IS ta kashe a bikin Afghanistan ya kai 26
2018-06-17 16:20:46 cri

A kalla mutane 26 ne suka mutu a lardin Nangarhar na gabashin kasar Afghanistan a harin kunar bakin wake wanda aka kai cikin wata mota kan taron jama'a a lokacin da suke gudanar da bukukuwan sallar Idi bayan yarjejeniyar tsakaita bude wuta da aka cimma.

Wani shafin yanar gizo na Amaq dake da nasaba da kungiyar dake fafutukar kafa daular muslunci ta IS wanda ta wallafa ta shafin intanet a harshen Larabci, ta yi ikirarin daukar alhakin kaddamar da harin wanda ya faru a wani yanki mai yawan jama'a dake birnin Jalalabad.

Daga cikin wadanda suka mutu, akwai mayakan kungiyar Taliban, fararen hula da kuma jami'an tsaron kasar Afghanistan. Wasu mutane 54 sun jikkata a harin.

Gwamnatin Afghanistan da mayakan Taliban sun cimma yarjejeniyar tsakaita bude wuta domin a samu damar gudanar da shagulgulan bikin karamar salla, biki na biyu mafi girma na mabiya addinin musulunci.

Tun da farko a ranar Asabar, a wani abu mai ban mamaki, an ga wasu daruruwan mayakan Taliban suna shiga wasu manyan biranen kasar Afghanistan domin yi ziyara da kuma gudanar da bukukuwan sallar Idi tare da 'yan uwansu.

Ministan cikin gida na Afghanistan Waiz Ahmad Barmak, ya gana tare da tattaunawa da mayakan na Taliban a yammacin birnin Kabul a ranar Asabar din, kamar yadda kafafen yada labaran kasar suka ba da rahoto.

Haka zalika a ranar Asabar, shugaban kasar Afghanistan Ashraf Ghani ya yanke shawarar tsawaita wa'adin yarjejeniyar tsakaita bude wutar, wanda ake sa ran zai kare a ranar Talata mai zuwa, zuwa wani lokacin da ba'a tabbatar da shi ba.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China