in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rasha ta bukaci a saukakawa Koriya ta arewa takunkumi
2018-06-17 16:26:52 cri

Kasar Rasha ta bukaci da a saukakawa Koriya ta arewa takunkumi, bayan da ta amince da kudurin raba zirin Koriya da makaman kare dangi.

Da take tsokaci game da hakan ga wani taron manema labarai, kakakin ma'aikatar harkokin wajen Rasha Maria Zakharova, ta ce gudanar da sauye sauye game da takunkumin da kwamitin tsaron MDD ya kakabawa Koriya ta arewan, daya ne daga muhimman matakai na tabbatar da nasarar burin da aka sanya gaba, na kawar da makaman nukiliya daga zirin na Koriya.

Maria Zakharova, ta ce aiwatar da hakan zai yi matukar tasiri wajen warware matsalolin siyasa da ake fama da su, a yankin arewa maso gabashin nahiyar Asiya.

MDD dai ta kakabawa Koriya ta arewa takunkumin karya tattalin arziki ne, bayan gwajin makaman kare dangi irin sa na farko da kasar ya aiwatar a shekarar 2006. Kana kuma wasu karin kasashe ciki hadda Amurka, su ma suka kakabawa Koriyan takunkumi.

To sai dai kuma bayan ganawar shugaba Kim Jong Un na Koriya ta arewa, da takwaransa na Amurka Donald Trump a Talatar makon jiya a Singapore, kasashen biyu sun fidda sanarwar hadin gwiwa, wadda ke kunshe da aniyar su, ta kawar da makaman kare dangi daga zirin Koriya, yayin da kuma aka alkawartawa Koriya ta arewa samun cikakken tsaro.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China