in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Faransa ta lashe kofin kwallon kafar duniya na bana
2018-07-16 14:53:14 cri

Kasar Faransa ta doke Croatia da ci 4-2, a wasan karshe na cin kofin kwallon kafar duniya da aka buga a jiya Lahadi, inda Faransar ta dauki wannan kofi a karo na 2 bayan shekaru 20.

An buga wasan karshen na gasar cin kofin kwallon kafa na duniya da hukumar FIFA ke shiryawa na shekarar nan ta 2018, a filin wasanni na Luzhniki da ke birnin Moscown kasar Rasha.

A lokacin da babban alkalin wasa ya busa usir din kammala wasa, masu sha'awar kwallon kafa sama da dubu goma daga kasar Faransa sun fara ihu suna murna a filin wasanni na Luzhnik. A daidai wannan lokacin, 'yan wasan kasar Faransa sun fara gudu cikin filin wasannin don murna, yayin da 'yan wasan kasar Croatia suka rika kwanciya a kasa domin matukar gajiya da takacin rashin nasarar su.

Wannan ne dai lokacin kammala wasan karshe na gasar kwallon kafa ta cin kofin duniya ta shekarar 2018 a kasar Rasha, inda kasar Faransa ta zama zakara.

Hakika dai, kafin a kai ga zagayen karshe na gasar, an yi hasashen cewa, kungiyar kasar Croatia da ta kai zagayen karshe na gasar a karo na farko ita ce za ta lashe gasar, ganin yadda ta kokarta a farkon wasan karshe na gasar. Amma burinta bai kai ga cika ba, yanayin gasar ta sauya bayan kura kurai da 'yan wasan ta suka yi. A minti na 18 na gasar, kungiyar Faransa ta samu kwallon farko bayan da dan wasan kasar Croatia Mandzukic ya ci gidan su da ka. Kana a minti na 28 na gasar, dan wasan kasar Croatia Perisic ya farke wa kasar sa wannan kwallo, lamarin da ya sanya sassan biyu yin canjaras. Amma bayan mintoci goma kacal, sai Perisic ya yi wani kuskuren da bai kamata ba, wato ya taba kwallo da hannu, yayin da yake tsaron baya, lamarin da ya sa kungiyar Faransa ta samu damar bugun daga kai sai mai tsaron gida. Bayan 'dan wasan kasar Faransa Griezmann ya sa kwallo a raga, an ci gaba da taka leda da ci 2 da 1.

A karawa ta karshe, kungiyar Croatia da ke da niyyar kara sanya kwallo raga ta yi kura-kurai. Inda a minti na 59 da na 65, 'yan wasan kungiyar Faransa suka jefa karin kwallaye biyu a zaren Croatia. Amma a minti na 69, kungiyar Croatia ta samu damar jefa karin kwallo daya a ragar Faransa. Hakan ya sa aka kai ga tashi wasan da ci 4 da 2.

Dan wasan kasar Faransa Griezmann wanda ya samu lambar yabo ta 'dan wasa mafi nagarta cikin wasan ya bayyana bayan gasar, cewar

"lallai wannan wata gasa ce mai matukar walaha, amma mun cimma nasara a karshe bisa kokarinmu, lallai ina farin ciki sosai."

Babban mai horoswa na kungiyar kasar Faransa Didier Deschamps ya taba cin kofin duniya na shekarar 1998 a matsayinsa na kyaftin din kungiyar 'yan wasan Faransa. Ya sake cin kofin a wannan karo a matsayinsa na babban mai horaswa. Lamarin da zai taimaka masa wajen tabbatar da babban matsayinsa a dandalin wasan kwallon kafa na Faransa. Bayan gasar, Deschamps ya yi murna matuka har ya kusa kuka, ya ce,

"kungiyarmu ta nuna basira da karfin gwiwa a lokacin gasar, mun cimma burinmu. Ina alhafari da su, sabo da cimma nasara ba abu ne mai sauki ba. Mun kawar da bakin cikin mu na gaza zama zakara a cin zakarun kasashen Turai yau da shekaru biyu da suka wuce. Dukkan 'yan kungiyarmu sun samu nasara. Ba shakka mu ne mafi kwarewa a duniya."

A nasa bangaren, babban mai horaswa na kungiyar Croatia Zlatko Dalić ya ce, ya yi alfahari da 'yan wasan sa, duba da yadda suka yi iyakacin kokarinsu har zuwa karshe, kuma za su koma gida kamar yadda masu cikakkiyar nasara ke cike da alfahari.

Bayan wasan karshe na gasar, an bayar da lambobin yabo na gasar cin kofin duniya ta wannan karo, inda Luka Modric, 'dan wasan kasar Croatia ya samu lambar yabo ta Kwallon Zinari, wadda ta alamta shi a matsayin dan wasa mafi yin fice a gasar, yayin da mai bugawa na kasar Birtaniya Harry Kane ya samu lambar yabo ta Takalmin Zinari, sakamakon kwallo shida da ya zura a raga a gasar ta bana.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China