in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wasan roller a kasar ta Sin
2018-08-06 18:26:12 cri

A nan kasar Sin wasan roller ya dade yana samun karbuwa, don ina iya tunawa da lokacin da nake makaranta, dalibai su kan tafi filayen wasan roller skating domin a yi wasa tare, sa'an nan zuwa yanzu na kan ga kananan yara da yawa wadanda shekarunsu ba su wuce 3 zuwa 4 ba, sana fara shiga darasin koyon fasahar wasan roller, inda yaran suke sanye da hular musamman ta ba da kariya, da sauran kayayyakin kariya a gabobin jikin su, suna gwada wasu motsi na musamman bisa yadda malamansu suka nuna musu.

Musamman ma a wannan lokacin da kasar Sin take kokarin shirin karbar bakuncin wasannin Olympics na lokacin hunturu a shekarar 2020, gwamnatin kasar tana kokarin yayata wasanni masu alaka da kankara tsakanin jama'a. Sa'an nan wasan roller, duk da cewa ba wani wasa ne da ake gudanar da shi kan filin kankara ba, amma mun san asalinsa shi ne wasan skating, wani wasan tsere na musamman da ake gudanar da shi kan kankara. Daga bisani don biyan bukatun ci gaba da wasan skating a lokacin da babu kankara, aka kirkiro fasahar sanya wili ko taya a karkashin takalmar skating, wadda ta zamo wasan roller skating ke nan. Saboda haka dukkan fasahohin da ake da su wajen gudanar da wasan roller skating sun yi kama da na wasan skating. Dalilin haka, wasan roller ya kara samun damar yaduwa tsakanin al'ummun kasar Sin a wannan lokacin da muke ciki. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China