in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin da Afirka sun samu sabon ci gaban hadin gwiwar hada-hadar kudi
2018-08-15 10:09:43 cri

Yayin taron koli na Johannesburg na dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afrika da ya gudana a watan Disamba na shekarar 2015, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya sanar da daga matsayin dangantakar Sin da Afrika zuwa dangantakar hadin gwiwa ta abota bisa manyan tsare-tsare a dukkanin fannoni, kuma ya gabatar da shirin hadin gwiwa guda goma, dake shafar fannin masana'antu, aikin noma na zamani, ababen more rayuwa, hada-hadar kudi, samun bunkasuwa tare da kiyaye muhalli, ciniki da zuba jari cikin sauri, rage talauci, kiwon lafiya, al'adu, zaman lafiya da tsaro da dai sauransu. Wadannan shirye-shirye sun shata wata taswirar kara inganta hadin kan Sin da Afrika a nan gaba, kuma ya bude wani sabon babi na sabuwar dangantakar bangarorin biyu.  

A gabannin taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka da za a yi a nan birnin Beijing, za mu yi muku bayani kan sabon ci gaban da aka samu a fannin hada-hadar kudi yayin da sassan biyu suke gudanar da hadin gwiwa a tsakaninsu.

Darektan cibiyar nazari kan harkokin kasar Sin ta jami'ar Dar es Salaam ta kasar Tanzaniya Humphrey P. B. Moshi yana ganin cewa, sakamakon da kasar Sin ta samu ya samar da damammaki ga kasar da ta sauya daga matsayinta na babbar kasa mai jawo hankalin masu zuba jari zuwa babbar kasa wadda take zuba jari a kasashen ketare, kasashen Afirka suna cin babbar gajiya daga hadin gwiwar harkar hada-hadar kudi dake tsakaninsu da kasar Sin.

Yana mai cewa, "A cikin shekaru 40 da suka wuce, gwamnatin kasar Sin tana kokarin gudanar da hadin gwiwa tsakaninta da sauran kasashen duniya, haka kuma ta sa kaimi kan cinikayya da zuba jari, lamarin da ya amfanawa kasashen Afirka, ciki har da kasar ta Tanzaniya, kana babban ci gaban da kasar Sin ta samu a cikin wadannan shekaru ya samar wa kasar Sin ita kanta damammaki na zuba jari a kasashen ketare, musamman ma a kasashen Afirka wadanda ke matukar bukatar samun ci gaba."

Mataimakin shugaban jami'ar nazarin harkokin tattalin arziki da cinikayyar waje ta kasar Sin Ding Zhijie na ganin cewa, hadin gwiwa a harkar hada-hadar kudi dake tsakanin Sin da Afirka yana da muhimmanci matuka ga sassan biyu. A cewarsa: "Makomar hadin gwiwar hada-hadar kudi dake tsakanin Sin da Afirka tana da haske, da farko dai, a halin yanzu, yawancin kasashen Afirka suna fama da matsalolin da kasar Sin ta gamu da su yayin da take kokarin samun ci gaba a cikin shekaru 40 da suka gabata, haka kuma matsayin bunkasar tattalin arzikinsu kusan sun yi kama da juna, a don haka kasashen Afirka suna iya koyon fasahohin da kasar Sin ta samu, na biyu, adadin kudaden da aka adana a cikin bankunan kasar Sin suna da yawan gaske, amma kasashen Afirka suna fama da karancin kudi yayin da suke kokarin raya tattalin arzikinsu, idan kasar Sin ta kara zuba jari a kasashen Afirka, ko kuma sassan biyu suka gudanar da hadin gwiwa dake tsakaninsu yadda ya kamata, hakan zai sa sassan biyu su samu moriyar juna a wannan fanni, na uku, idan aka kara yin amfani da kudin Sin RMB a fadin duniya, musamman ma yayin da ake gudanar da cinikayya tsakanin Sin da Afirka, lamarin zai taimaka matuka wajen ci gaban tattalin arzikin kasashen Afirka baki daya."

Sakamakon ingantuwar hadin gwiwar hada-hadar kudi tsakanin Sin da Afirka, sannu a hankali tsarin hadin gwiwarsu ma ya kyautata, kana kasar Sin ta kafa wasu hukumomi na musamman domin kara inganta wannan hadin gwiwa.

Mataimakin shugaban bankin shige da fice na kasar Sin Xie Ping ya bayyana cewa, a halin da ake ciki yanzu, adadin ayyukan da ake gudanarwa a kasashen Afirka 47 da yake samarwa rancen kudi a kasashen ya kai sama da 600, yunkurin gwamnatin kasar Sin ya ciyar da hadin gwiwar dake tsakaninta da kasashen Afirka gaba daga duk fannoni.

A bayyane ne hadin gwiwar dake tsakanin bankunan Sin da Afirka yana taka muhimmiyar rawa kan hadin gwiwar hada-hadar kudi tsakanin sassan biyu. A shekarar 2008, bankin masana'antu da kasuwancin kasar Sin ya kashe kudi dalar Amurka biliyan 5 da miliyan 500 wajen sayen kaso 20 bisa dari na hannun jarin bankin Standard na kasar Afirka ta Kudu da har ya zama mafi yawan mallakar hannun jarin bankin.

Mataimakin babban wakilin bankin masana'antu da kasuwancin kasar Sin dake wakilci a Afirka Sun Gang ya bayyana cewa, makasudin sayen hannun jarin bankin Standard na Afirka ta Kudu shi ne domin kara zurfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu, amma ba domin kara samun riba kawai ba. A cewarsa: "Muna gudanar da hadin gwiwa a fannoni biyu ne a kasashen Afirka, mu kan zuba jari kai tsaye kan wasu manyan ayyuka, kamar gina hanyoyin mota ko gina tashar samar da wutar lantarki, ban da wannan kuma, mu kan samar da rancen kudi ga kamfanonin kasashen Afirka ta hanyar gudanar da hadin gwiwa da bankunan kasashen."(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China