in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi babban taron hadin-gwiwar Sin da Afirka ta fannin kiwon lafiya na shekara ta 2018 a Beijing
2018-08-17 20:29:27 cri

Yau Jumma'a, a birnin Beijing, an kaddamar da babban taron hadin-gwiwar Sin da Afirka ta fuskar kiwon lafiya na shekara ta 2018, inda mahalarta taron suka cimma daidaito cewa, Sin da Afirka za su iya fadada hadin-gwiwarsu a fannonin da suka shafi samar da ingantaccen kiwon lafiya da bullo da tsarin kiwon lafiya dake iya tinkarar matsaloli daban-daban da kuma inganta lafiyar jama'a.

Jami'an hukumomin kiwon lafiya da kwararru da masana da wakilai na kungiyoyin kasa da kasa sama da dari uku daga kasar Sin da kasashen Afirka 36 ne suka halarci taron.

Mataimakiyar darektan hukumar kula da harkokin kiwon lafiya ta kasar Sin Madam Cui Li ta ce, baya ga hadin-gwiwa a tsoffin hanyoyi, a halin yanzu kasar Sin da kasashen Afirka na kokarin lalubo sabbin hanyoyi na karfafa hadin-gwiwa a fannin kiwon lafiya.

Cui ta ce, kasar Sin da wasu kasashen Afirka guda shida, ciki har da Cape Verde da Zimbabwe suna aiwatar da ayyukan bada misali na inganta lafiyar mata da yara kanana, da karfafa ayyukan gina cibiyoyin kula da lafiyar mata da kananan yara, da horas da kwararru a wadannan fannoni. Haka kuma, kasar Sin na yin tiyatar zuciya ga mutanen da suke da bukata a Ghana, da taimakawa kasar wajen horas da kwararru da masana a fannin kula da zuciya da jijiyoyi.

Shi ma a nasa bangaren, ministan kiwon lafiya na tarayyar Najeriya, Isaac Adewole ya ce, an samu dimbin nasarori wajen inganta hadin-gwiwar Sin da Afirka ta fuskar kiwon lafiya. Adewole ya ce, kasar Sin ta taimakawa Najeriya wajen kafa cibiyar hana yaduwar cututtuka a kasar, kuma Najeriya ta godewa kasar Sin saboda wannan taimako, abun da ya sa adadin mutanen da suka kamu da cututtuka da yawan mace-mace duk suka ragu a kasar. (Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China