Wakilai daga kasashen Afirka da kungiyar tarayyar Afirka wato AU da kuma kasar Sin sun yi kira da a karfafa hadin-gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa, da zuba karin kudade, da kara mai da hankali wajen kula da lafiyar mata da yara kanana, ta yadda za'a rage yawan mace-macen jariran da aka haifa.
Wata babbar jami'a daga kwamitin kula da harkokin kiwon lafiya ta kasar Sin Madam Song Li ta ce, Sin na fatan yayata nasarorin da ta samu a fannin inganta lafiyar mata da yara kanana ga kasashen Afirka, a wani mataki na bayar da gudummawarta ga inganta lafiyar mata da yara kanana a fadin duniya baki daya. (Murtala Zhang)