Wu Qian ya jaddada cewa, kasar Sin ta dade tana neman samun ci gaba cikin lumana, da bayar da gudummawarta wajen tabbatar da zaman lafiya da tabbatar da kiyaye doka da oda a fadin duniya baki daya. Ya ce a 'yan shekarun nan, sojojin kasar Sin na nuna himma da kwazo wajen shiga ayyukan soja a kasashen waje, ciki har da kiyaye zaman lafiya, da bada kariya ga ayarin jiragen ruwa da kuma gudanar da ayyukan ceto. Kasar Sin na kara sauke nauyin dake wuyanta, da tabbatar da zaman lafiya da tsaro a duniya, kuma gudummawa gami da kokarin da ta yi sun sa ta samu yabo daga kasashen duniya.
Bugu da kari, Wu ya jaddada cewa, Taiwan wani yanki ne da ba za'a iya raba shi daga kasar Sin ba. (Murtala Zhang)