in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tsohon Sakatare Janar na MDD ya rasu yana da shekaru 80
2018-08-18 21:06:55 cri

Gidauniyar Kofi Annan dake da mazauni a Geneva, ta sanar da mutuwar tsohon Sakatare Janar na MDD, kuma wanda ya taba samun lambar yabo ta Nobel kan zaman lafiya, wato Kofi Annan mai shekaru 80.

An haifi Kofi Annan ne ranar 9 ga watan Afrilun 1938 a Ghana. Ya kuma kasance Sakatare Janar na MDD na 7, daga watan Junairun 1997 zuwa Disamban 2006. Da shi da MDD ne suka samu lambar yabo ta Nobel kan zaman lafiya a shekarar 2001.

Shi ne Shugaba, kuma wanda ya asassa Gidauniyar Kofi Annan, haka zalika, shi ne shugaban The Elders, kungiyar masu fafutukar tabbatar da zaman lafiya da marigayi Nelson Mandela ya kafa.

Da take bayyana Kofi Annan a matsayin 'Da ga kasar Ghana', Gidauniyar Kofi Annan, ta bayyana cikin sanarwar da ta fitar cewa, marigayin ya jajirce wajen ganin ci gaban nahiyar Afrika, haka kuma, ya shiga cikin shirye-shirye, ciki har da shugabantar kwamitin raya Afrika da kuma kungiyar inganta ayyukan noma a Afrika ta Alliance for a Green Revolution in Africa.

Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres, ya bayyana bakin cikin mutuwar Annan, ya na mai bayyana shi a matsayin abun misali na ayyukan kwarai.

Shi ma Shugaban kasar Ghana, ya bayyana jimami dangane da mutuwar, inda ya bayyana marigayin a matsayin wanda ya yi ammana ga karfin 'yan Ghana na samun nasara da ci gaba da kansu. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China