in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wang Yi ya tattauna ta waya da takwaransa na Turkiya
2018-08-19 16:20:18 cri

A jiya ne mamba a majalisar zartarwar kasar Sin kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi ya tattauna ta wayar da tarho da takwaransa na kasar Turkiya Mevlut Cavusoglu game da al'amuran da ke faruwa.

Yayin tattaunawar tasu, Wang Yi ya bayyana manufofi da matsayar kasar Sin kan yadda za ta raya alakarta da kasar Turkiya bisa manya tsare-tsare. Ya ce kasar Sin na goyon bayan matakan da Turkiya ke dauka na tabbatar da tsaro da zaman lafiya da raya tattalin arziki da jin dadin jama'a.

Jami'in na kasar Sin, ya kuma yi imanin cewa, a karkashin jagorancin shugaba Recep Tayyip Erdogan, al'ummar Turkiya za su hada kansu wajen ganin sun magance matsalolin da suke fuskanta a halin yanzu.

A nasa bangare, Cavusoglu ya jaddada cewa, Turkiya za ta magance kalubalen da take fuskanta, haka kuma a shirye kasarsa ta ke ta zurfafa tattauna bisa manyan tsare-tsare da kasar Sin, da fadada alakar moriyar juna, da kuma shiga a dama da ita wajen gina shawarar ziri daya da hanya daya.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China