in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Navas na Real Madrid zai bar Costa Rica don wasan sada zumunci
2018-08-30 10:48:23 cri
Mai tsaron ragar kungiyar wasan Real Madrid Keylor Navas ya koma kungiyar Costa Rica domin halartar wasannin sada zumunci tsakanin kungiyar da takwarorinta na Korea ta kudu da Japan, hukumar gudanarwar wasan kwallon kafan Costa Rica ne ta tabbatar da hakan.

Keftin kuma mai tsara wasanni Bryan Ruiz, da dan wasan tsakiya Celso Borges, da mai tsaron baya Giancarlo Gonzalez, da dan wasan gaba Marco Urena da mai tsaron baya Yeltsin Tejeda dukkansu basu cikin tawagar 'yan wasa 23 yayin da kociya na rikon kwarya Ronald Gonzalez ya sauya matasan 'yan wasan na Asiya.

Wasan shine zai kasance irinsa na farko da Costa Rica zata gudanar a wannan kakar wasanin, tun bayan kammala gasar cin kofin duniya ta kasar Rasha, inda aka yi waje da kungiyar wasan a zagayen farko bayan ta rasa wasanninta biyu da kuma konnen doki data tashi dashi a wasanta guda.

"Mun zanta da dukkan 'yan wasa, wasu daga cikinsu basu dawo kungiyoyin wasansu ba har ya zuwa ranakun 15 ko 22 ga wata bayan kammala gasar cin kofin duniya," inji Gonzalez.

Costa Rica zata taka leda da Koriya ta kudu a Goyang ranar 7 ga watan Satumba, sannan bayan kwanaki hutu ta fafata da Japan.

An nada Gonzalez a matsayin kociya na rikon kwarya bayan an sallami Oscar Ramirez a watan Yuli.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China