in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ghana ba ta samu sanarwar dage wasan ta da Saliyo ba
2018-10-11 18:53:03 cri

Kungiyar kwallon kafar kasar Ghana ta ce kawo yanzu, bata samu wata sanarwa daga hukumar kwallon kafar nahiyar Afirka ta AFCON, dake bayyana dage wasan nema gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar na badi, da kungiyar za ta buga da Saliyo ba.

An dai shirya buga wasan tsakanin Black Stars ta Ghana da takwararta ta Saliyo a ranar Alhamis mai zuwa. To sai dai kuma wasu rahotanni na cewa, a ranar Juma'ar karshen makon jiya, hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta dakatar da kungiyar kwallon kafar kasar Saliyo, saboda zargin tsoma hannun gwamnatin kasar cikin harkokin kungiyar.

Da yake karin haske game da wannan batu ga manema labarai, kakakin kwamitin daidaita harkokin wasanni a Ghana Dan Kweku Yeboah, ya ce kawo yanzu ba su samu cikakken bayani game da dage wasan su da Saliyo daga hukumar CAF ba.

Ya ce "hukumar FIFA ko CAF ba su bayyana mana dage wasan na gaba ba. Mun kira mukaddashin shugaban wasanni ta FA, wanda ya tabbatar mana cewa za mu buga wasan kamar yadda aka tsara.

Mr. Yeboah ya kara da cewa, 'yan wasa za su isa filin atisaye a ranar Lahadi, su kuma fara horo a ranar Litinin, gabanin wasan da za a buga a filin wasa na Baba Yara dake birnin Kumasin kasar ta Ghana.

Jami'in ya kara da cewa, "ba za mu dakatar da zuwan 'yan wasan mu ba, saboda ba mu kai ga samun cikakken bayanin hakan daga CAF ba. Kuma ita kan ta hukumar FIFA na iya sauya matsaya gobe ko jibi, kamar dai yadda hakan ta faru a Najeriya.

Ghana na matsayi na daya a jadawalin rukuni na F da maki 3, ko da yake sauran kungiyoyin dake rukunin ma suna da maki uku uku ne, sakamakon kunnen doki da suka buga a wasannin su da suka gabata.

Za dai a buga gasar cin kofin nahiyar Afirka na shekarar 2019 wanda hukumar CAF ke shiryawa ne a kasar Kamaru, tsakanin wasannin Yuni zuwa Yulin shekara mai zuwa.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China