in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Asisat Oshoala: 'yar wasan kwallon kafa mafi kwarewa a nahiyar Afirka dake neman cimma burinta a kasar Sin
2018-10-20 20:34:03 cri

 

Birnin Dalian wani birni ne dake dab da bakin teku na kasar Sin, inda ake samun muhalli mai ni'ima. A kan wani filin wasa dake cibiyar wasannin motsa jiki ta birnin, wasu 'yan mata masu sanye da riga mai launin ja da fari suna buga kwallon kafa. Cikinsu akwai wata doguwar matashiya bakar fata, wadda take gudu cikin sauri, tare da sarrafa kwallo da kyau, har ma motsinta ya sa wani kocin dake tsaye a gefe ke ihu don nuna mata yabo. To, wannan kungiyar dake taka kwallo ita ce kungiyar wasan kwallon kafa ta Dalian Quanjian FC, wadda ta taba zama zakarar gasar kwararrun kuloflikan wasan kwallon kafa na 'yan matan kasar Sin karo da dama. Yayin da wannan 'yar Afirka ta kasance kwararriyar 'yar wasa da kulob din ta samu daga kasar Najeriya, kuma 'yar wasan kwallon kafa mafi kwarewa a nahiyar Afirka, Asisat Oshoala.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China