in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tsanantar rikicin ciniki zai kawo hadari ga tattalin arzikin duniya
2018-10-19 11:15:20 cri
Babban direktan hukumar ciniki ta duniya wato WTO Roberto Azevêdo ya yi kashedi a birnin London a ranar 17 ga wata cewa, tsanantar rikicin ciniki zai kawo hadari ga tattalin arzikin duniya, cinikin duniya yana fuskantar barazana.

Azevêdo ya bayyana yayin da yake halartar wata liyafa a birnin London cewa, masanan tattalin arziki na hukumar WTO suna yin bincike kan yiwuwar tasirin rikicin ciniki, ciki har da tasirin da za a samu idan rikicin ciniki ya barke a dukkan fannoni. Bisa hasashen da suka yi, idan aka lalata dukkan hadin gwiwar cinikayya a tsakanin kasa da kasa, saurin bunkasuwar cinikin duniya zai ragu da kashi 17 cikin dari, yawan saurin bunkasuwar GDP na dukkan duniya zai ragu da kashi 1.9 cikin dari, kana mutane fiye da miliyan daya za su rasa ayyukansu.

Azevêdo ya kara da cewa, don tabbatar da moriyar dukkan mutanen duniya, kasa da kasa suna da alhakin sassauta halin rikicin ciniki, ya kamata a kara yin shawarwari a tsakanin bangarori da dama ko bisa tsarin kungiyar WTO, domin neman samun hanyar daidaita matsalar bisa tsarin ciniki a tsakanin bangarori daban daban. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China