in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude bikin baje-kolin kayayyakin kasa da kasa a birnin Yiwu na kasar Sin
2018-10-22 10:42:31 cri

An kaddamar da bikin baje-kolin kayayyakin kasa da kasa karo na 24 a birnin Yiwu na lardin Zhejiang dake gabashin kasar Sin. An kafa rumfuna 4,136 a wajen bikin baje-koli mai fadin murabba'in mita dubu dari, inda kamfanoni 2150 daga kasashen Amurka, da Rasha, da Jamus, da Portugal, gami da na larduna da jihohi, da birane 26 na kasar Sin suka hallara.

Birnin Yiwu yana tsakiyar lardin Zhejiang, inda ake samun kasuwar cinikin kananan kayayyaki mafiya girma a duk fadin duniya. An fitar da kayayyaki daga kasuwar zuwa kasashe da yankuna sama da 210 na duniya. A bana, adadin kamfanonin da ba na birnin Yiwu ba, wadanda suka halarci bikin ya karu idan aka kwatanta da na bara, inda kamfanoni kimanin 1700 suka zo daga sauran yankunan da suka halarci bikin bana, adadin da ya dauki kashi 75 bisa dari na dukkan rumfunan bikin.

Har wa yau, domin kara kyautata tsarin bikin baje-kolin na bana, an kebe wasu sassan baje-kolin kayayyaki masu sigar musamman guda 14, ciki har da na baje-kolin jakunkuna da na kayayyakin da ake saye da sayarwa ta kafar Intanet.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China