Shugaban Xi ya bayyana haka ne cikin wata wasikar da ya rubuta dangane da karrama wasu 'yan kasuwa da aka yi, wadanda suka bada gudunmawa ga aikin yaki da talauci
Cikin wasikar, shugaban ya yaba kwarai da jajarcewar 'yan kasuwar ga shirin yaki da talauci.
Ya ce ya yi murna da ganin karuwar adadin 'yan kasuwa dake sauke nauyin da ya rataya a wuyansu na taimakawa al'umma, inda suke dukufa ga aikin yaki da talauci da taimakawa marasa galihu.
Sama da 'yan kasuwa 60,000 ne suka shiga gangamin yaki da talauci da aka yi wa lakabi da "'yan kasuwa 10,000 masu taimakawa kauyuka 10,000" tun bayan kaddamar da shi a watan Oktoban 2015, inda aka karrama 100 daga cikinsu a farkon watan nan. (Fa'iza Mustapha)