in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wasan shawagi da wani irin tufafi na musamman mai siffar fika-fikai
2018-11-23 09:39:06 cri


Game da tarihin wasan nan na shawagi da wani tufafi na musamman, an san cewa gwaji na farko a wannan fanni, wato shawagi da wani irin tufafi, ya faru ne a shekarar 1912, kuma mutum da ya yi gwajin shi ne wani madinki mai shekaru 33 a duniya na kasar Faransa, Franz Reichelt. Ya tsara wani irin tufafin da ya hada da laimar sauka da kuma fika-fikai, wanda tsarinsa ya yi kama da na tufafin Wingsuit na zamani. Sa'an nan ya nemi hukumar birnin Paris don ta ba shi izini gudanar da gwaji kan hasumiyar Eiffel Tower, inda ya yi karyar cewa zai yi gwaji da wani mutum-mutumi ne, wato zai hada tufafin da ya tsara da wani mutum-mutumi, sa'an nan a jefa su daga saman Eiffel Tower, amma a hakika shi da kansa ne ke shirin gwajin wannan tufafi. A waccan rana, ya tsaya kan hasumiyar Eiffel Tower mai matukar tsayi, sa'an nan ya yi tsalle ya sauka. Amma laimar sauka dake cikin tufafinsa ba ta bude ba. Kansa ya ci karo da kasa, wannan ya sa ya mutu nan take. Har ma nauyin jikinsa ya sa aka samu wani rami a kasa. Duk da cewa shi Franz Reichelt bai yi nasara wajen samar da tufafin da zai taimakawa mutane shawagi ba. Amma bisa gudunmowar da ya bayar, aka ci gaba da kokarin samar da wannan irin tufafi na musamman.

Karo na farko da aka fara amfani da wani Wingsuit shi ne a shekarar 1930, inda wani saurayi na kasar Amurka Rex Finney ya sanya tufafin na musamman don daidaita yadda yake shawagi a sama, bayan da ya yi tsalle daga wani jirgin sama da laimar sauka. A wancan zamani, an tsara tsoffin tufafi na Wingsuit ne da yadi, siliki, itace, da karfe. Ba su da cikakken inganci, duk da haka wasu kwararru sun yi amfani da tufafin wajen shawagi har nisan wasu kilomita.

Zuwa tsakiyar shekarun 1990, Patrick Gayardon, shi ma wani dan kasar Faransa ne, ya tsara tufafi na Wingsuit na zamani. Sa'an nan a shekarar 1997, wani dan kasar Bulgaria Sammy Popov ya tsara wani irin tufafi na Wingsuit, wanda ke da fiffike mafi girma tsakanin kafafuwan mutum, da kuma fika-fikai masu tsayi a hannayensa. An gwada tufafin da na'urar musamman ta "wind tunnel", sa'an nan an gwada shawagi da tufafin a shekarar 1998, inda aka samu nasara. An ce, da wannan tufafi, an samu rage saurin saukowar mutum zuwa kilomita 30 bisa awa daya, yayin da saurin ci gabansa ya kai fiye da kilomita 300 bisa awa daya. Sai dai saboda wasu dalilai, shi Popov bai samu samar da wannan tafafin da ya tsara ga kasuwa ba. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China