A kwanakin baya, ba sau daya ba kuma ba sau biyu ba, rundunar sojan Amurka ita ma ta yi wasu kalamai dangane da batutuwan da suka shafi Taiwan. Babu shakka dukkan wadannan abubuwan da Amurka ta yi, za su yi illa ga dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka da kuma alakar dake tsakanin babban yankin kasar Sin da lardin Taiwan, har ma su kawo barazana ga zaman lafiya da kwanciyar hankali. Amma irin martanin da hukumar Taiwan dake karkashin jagorancin Tsai Ing-wen ta mayar, za ta janyo hadari ga lardin Taiwan.(Murtala Zhang)