in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta shawarci kasashe masu ruwa da tsaki a yarjejeniyar INF da su warware sabani ta hanyar tattaunawa
2018-10-22 20:17:22 cri
Sin ta shawarci kasashe masu ruwa da tsaki, a yarjejeniyar hana kerawa da gwajin makaman nukiliya masu cin gajere da matsakaicin zango wato yarjejeniyar INT, da su warware sabanin dake tsakanin su ta hanyar tattaunawa da shawarwari.

Da take tsokaci game da hakan, yayin taron manema labarai da ya gudana a yau, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying, ta ce sam bai dace kasar Amurka, ta janye daga yarjejeniyar ta INF ba.

Hua Chunying ta kara da cewa, yarjejeniyar tana taka muhimmiyar rawa, wajen dakile ci gaba da yaduwar makamai masu cin gajere da matsakaicin zango, wadda aka cimma tsakanin tsohuwar tarayyar Soviet, da Amurka a yayin yakin cacar baka. A cewar ta, janyewar Amurka zai haifar da mummunan tasiri a sassa daban daban.

A ranar Asabar ne dai shugaba Donald Trump na Amurka, ya ayyana aniyar gwamnatin sa na ficewa daga wannan yarjejeniya, wadda aka sanyawa hannu tun a shekarar 1987. Ta kuma shafi daukar matakan kauda kanana, da matsakaitan makamai masu linzami, tsakanin kasashen tsohuwar tarayyar Soviet da Amurka.

Trump dai ya zargi Russia da karya ka'idojin yarjejeniyar, yana mai cewa dole ne Amurka ta ci gaba da kera wadannan makamai, muddin kasashen Sin da Rasha, basu su dauki matakan dakatar da kera irin wadannan makamai ba.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China