in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin kundin tsarin mulkin kasar Kamaru ya fara sanar da sakamakon babban zaben kasar
2018-10-22 20:28:35 cri
A yau Litinin ne kwamitin kundin tsarin mulkin kasar Kamaru, ya fara fayyace sakamakon zaben shugaban kasar da aka gudanar a ranar 7 ga watan nan.

Shugaban kwamitin mai shari'a Clement Atangana, shi ne ya bayyana hakan yayin bikin fara bayyana sakamakon zaben, a birnin Yaounde fadar mulkin kasar.

Mr. Atangana ya ce za a fara ne da bayyana sakamakon zaben yankuna, da na sassa, da kananan sassan kasar. Sai kuma na kuri'un da aka kada a wajen kasar, kafin daga bisani a bayyana wanda ya lashe zaben baki daya.

Mai shari'a Atangana ya ce zaben ya cika sharuddan kasancewa mai inganci da tsafta, kuma kwamitin kundin mulkin kasar ya gamsu da shi.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China