in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sama da wakilai 500 ne za su halarci taron dandalin Xiangshan na birnin Beijing
2018-10-22 21:25:12 cri
Sama da wakilai 500 daga kasashe 67 da ma kungiyoyi 7 ne za su halarci taron dandalin Xiangshan na birnin Beijing, a cewar mashirya dandalin na bana, wanda zai gudana tsakanin ranekun 24 zuwa 26 ga watan nan.

Taken taron dai shi ne "samar da sabon yanayin hadin gwiwa a fannin tsaro bisa daidaito, da yarda da juna da hadin gwiwar cin moriya tare."

Ana sa ran mahalarta taron da suka kunshi mashiryansa, da masana da aka gayyata, za su maida hankali ga tattauna batun tsaro tsakanin kasa da kasa, da yaki da barazanar ta'addanci, da tsaron teku, da kuma hadin gwiwa a ayyukan wanzar da zaman lafiya na MDD.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China