in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Botswana zata karbi bakuncin kwallon teburi ta Afrika
2018-11-07 16:44:42 cri
A mako mai zuwa ne kungiyar kwallon teburi ta Botswana (BTA) zata karbi bakuncin gasar kwallon teburi mafi girma wanda za'a fafata tsakanin kasashen Afrika, wanda ake saran kasashen nahiyar 13 zasu halarta.

Gasar, wadda za'a gudanar a matakai na daidaiku, da na bibiyu, da kuma matakai na tawaga tawaga, gasar an budeta ne a ranar 5 ga watan Nuwamba a babban filin wasannin kwallon teburi dake Gaborone babban birnin kasar, kuma za'a kammala gasar a ranar 10 ga watan Nuwamba.

Kasashen da zasu shiga gasar wanda Botswana zata karbi bakuncinta sun hada da, Afrika ta kudu Zambia, Zimbabwe, Kenya, Saliyo, Burkina Faso, Tunisia, Madagascar, Comoros, Morocco, Gabon da kuma demokaradiyyar Kongo

An sahhalewa kowace kasa ta gabatar da 'yan wasa maza 3 mata 3.

Sai dai, kasar Botswana mai masaukin baki an lamince mata ta fitar da 'yan wasan maza 5 mata 5.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China