in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Makon kandagarkin gobara na duniya
2018-11-15 15:03:45 cri

An kirkiro makon kandagarkin aukuwar gobara ne a ranar 9 ga watan Oktoban shekarar 1911, da nufin tuna sama da mutane 250 da suka halaka sanadiyar mummunar gobarar da ta faru a birnin Chicagon kasar Amurka. 'Yan kwana-kwana sun shafe kusan sa' o'i 27 suna kokarin kashe gobarar da aka yi kiyasin cewa, ta lalata gidaje sama da dubu 17, baya ga tarin dukiyoyi da suka salwanta.

Bugu da kari, a kan yi amfani da wannan mako wajen Ilimantar da jama'a matakan riga kafin aukuwar gobara a gidajen kwana, ofisoshi,da wuraren sana'a da sauransu.

Ana kuma amfani da wannan rana wajen jinjinawa 'yan kwana-kwana bisa ga najimin kokarin da suke yi a fannin sanar da jama'a matakan riga kafin gobara da ma yadda suke gudanar da ayyukansu na kashe gobara a lokuta daban-daban.

Masana na bayyana gobara a matsayin babban bala'I ga duniya, wadda ke kaiwa ga asarar rayuka da dukiyoyi. Wannan ne ya sa kowa ce kasa ke kafa hukumar kashe gobara. Inda daga lokaci zuwa lokaci ta ke sanar da jama'a matakan kandagarki wannan bala'i. Akwai bukatar jama'a su guji jefar da guntun taba a ko'ina ko shan taba a kan gado da sauran su.

Bayanai na nuna cewa, a kowa ce rana, mutane bakwai ne ke mutuwa sanadiyar gobara. Don haka, idan kunne ya ji to gangan jiki ya tsira. (Ahmed, Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China