in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin na kokarin aiwatar da "yarjejeniyar Paris" domin tinkarar sauyin yanayi
2018-11-27 11:49:20 cri

A farkon watan Disamba mai kamawa ne, za a yi taro karo na 24 tsakanin bangarori wadanda suka sanya hannu kan "yarjejeniyar tinkarar sauyin yanayi ta MDD" a garin Katowice na kasar Poland, inda za su kada kuri'a kan matakan da za a bi wajen aiwatar da "yarjejeniyar Paris". A jiya Litinin, Mr. Xie Zhenhua, wakilin musamman na kasar Sin wanda ke kula da batun sauyin yanayi ya bayyana a nan Beijing cewa, kasar Sin za ta ci gaba da tsayawa kan matsayin tinkarar sauyin yanayi, yana kuma sa ran za a kammala tattauna matakai filla filla domin aiwatar da "yarjejeniyar Paris" kamar yadda ya kamata.

Mr. Xie Zhenhua ya bayyana cewa, bangaren Sin yana fatan za a yi nasara a fannoni 3 a yayin taron tinkarar yanayin duniya na MDD da za a yi a kasar Poland, "A shekarar 2015 ne aka fara aiki da 'Yarjejeniyar Paris', kamar yadda aka umarta, ya kamata a kammala tattauna matakan aiwatar da yarjejeniyar. Sabo da haka, muna fatan za a bullo da wani tsarin tabbatar da aiwatar da 'yarjejeniyar Paris' kamar yadda ake fata. Sannan muna fatan a shirya taron kara wa juna sani na Talanoa, inda kowane bangare zai gabatar da sakamako mafi dacewa na tinkarar sauyin yanayi domin ingiza kowane bangare ya sauya salon neman ci gaba. Bugu da kari, wani muhimmin abu shi ne batun kudi. Muna fatan kasashe masu arziki za su riga sauran kasashe rage fitar da abubuwan dake gurbata muhalli da suke fitarwa. Sannan a binciki yadda ake tattara dala Amurka biliyan 100, ta yadda za a kai ga kafa wani kyakkyawan tushe ga aikin aiwatar da 'yarjejeniyar Paris' da za a yi bayan shekarar 2020 domin kokarin cimma buri na dogon lokaci kan tinkarar sauyin yanayi."

Mr. Xie Zhenhua ya kara da cewa, kasar Sin ba za ta canja matsayinta kan tinkarar sauyin yanayi da ganin an aiwatar da "yarjejeniyar Paris" ba. "Mun yi alkawarin cewa, nan da shekarar 2020, yawan abubuwan dake dumama yanayin duniya da za mu fitar zai ragu da kashi 40 zuwa kashi 45 cikin dari. Yawan makamashi maras gurbata muhalli da za mu yi amfani da shi zai karu zuwa kashi 15 cikin dari daga cikin dukkan makamashin da muke amfani da su. Bugu da kari, yawan gandun daji zai karu da kubik mita biliyan 1.3. Ya zuwa karshen shekarar 2017, yawan sinadarin dake dumama yanayin duniya da muke fitarwa ya ragu da kashi 46 cikin dari. Yawan makamashi maras gurbata muhalli da muke amfani da shi ya kai kashi 13.8 cikin dari, tabbas za mu iya cimma burinmu a shekarar 2020. Yawan gandun daji ya riga ya karu da kubik mita biliyan 2.1, wato mun riga mun cimma burin da ya kamata mu cimma nan da shekarar 2020."

Matakan tinkarar sauyin yanayi da kasar Sin ta dauka sun taimaka wajen raya tattalin arziki da zamantakewa mai inganci. Alkaluman da aka fitar na nuna cewa, tun daga shekarar 2005 zuwa yanzu, jimillar makamashin da kasar Sin ta yi tsimi ta kai fiye da rabin makamashin da aka yi tsiminsu a duk duniya. Bugu da kari, yawan dajin da kasar Sin ta dasa ya kasance a kan gaba a duk duniya. Sakamakon haka, yanzu yawan dazukan da kasar Sin take da su ya kai kashi 22 cikin dari na dukkan girman yankunanta.

Mr. Xie Zhenhua ya jaddada cewa, ra'ayin tinkarar sauyin yanayin duniya sun alamta cewa, dan Adam na fatan neman samun ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba, kuma dole ne a sauya salon neman ci gaba bisa sabbin fasahohin zamani da ake kirkirowa. Yanzu duk duniya ta amince da wannan ra'ayi. Sakamakon haka, bangaren Sin yana fatan a lokacin da ake aiwatar da "yarjejeniyar Paris" da kuma bullo da tsarin tabbatar da aiwatar da yarjejeniyar, ya kamata kowace kasa ta martaba duk wata ka'idar "yarjejeniyar Paris", ta yadda za a samu amincewa tsakanin kasa da kasa a fannin siyasa da kuma daukar matakan cimma duk wani buri a matakai daban daban wajen tinkarar yanayin duniya.

"Yanzu muna fatan kasashe masu arziki su cika alkawuran da suka dauka kamar yadda ya kamata. Wata muhimmiyar ka'idar dake cikin 'yarjejeniyar Paris', ita ce mataki da goyon baya su yi daidai da juna. Mataki shi ne matakin sassautawa da kuma na dacewa. Goyon baya shi ne ya kamata kasashe masu arziki su tallafa wa kasashe masu tasowa da kudi da kuma fasahohi, ta yadda kasashe masu tasowa za su inganta karfinsu a fannoni daban daban na tinkarar sauyin yanayin duniyarmu." (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China