Jami'in ya yi furucin ne yayin bikin bude taron karawa juna sani dangane da yanayin harkokin kasa da kasa da aikin diplomasiyya na kasar Sin a shekarar 2018. Ya kara da cewa, gwamnatin kasar Sin a ko da yaushe tana mai da hankali kan kula da lafiyar duk wani dan kasarta dake ketare, kuma za ta yi iyakacin kokarinta wajen ganin ta kare hakkin jama'ar kasar Sin, gami da tabbatar da yi musu adalci a duniya. (Bello Wang)