Tun daga yau Alhamis, za'a soma aiwatar da dokar da ta amince da shirya bikin tunawa da mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon kisan kiyashin da maharan kasar Japan suka yi a Nanjing a hukumance, dokar da ta kasance irinta ta farko da kasar Sin ta zartas kan bikin tunawa da mutanen. Dokar ta tanadi yadda za'a tallafawa mutanen da suka tsallake rijiya da baya a kisan kiyashin da aka yi a Nanjing, da matakan kula da wuraren da ake shirya bikin tunawar
A ranar 27 ga watan Fabrairun shekarar 2014, a yayin taro karo na bakwai na zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin karo na 12, aka zartas da wata doka, inda aka kebe ranar 13 ga watan Disambar kowace shekara a matsayin ranar tunawa da mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon kisan kiyashin da maharan Japan suka aikata a birnin Nanjing.(Murtala Zhang)